Kayode Fayemi: Ministan Buhari zaiyi murabus nan da mako daya

Nigeria to host 100 exploration companies at 2018 mining week

Fayemi, wanda ke neman kujerar gwamna na jihar Ekiti karkashin jam’iyyar APC ya bayyana hakan ne yayin da ya zanta da manema labarai a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Wani hazikin ministan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa zai aje aikin sa nan da mako daya domin mayar da hankalin ga kujerara siayasa da yake nema.

Ministan ma’adinai kuma tsohon gwamna, Dr. Kayode Fayemi a ranar Laraba, 16 ga watan Mayu yace zai yi murabus daga matsayinsa nan da mako guda.

Fayemi, wanda ke neman kujerar gwamna na jihar Ekiti karkashin jam’iyyar APC ya bayyana hakan ne yayin da ya zanta da manema labarai a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Yace akwai aiki sosai da zasuyi sannan kuma shi da sauran masu takara na kalon wannan zabe mai zuwa a matsayin hanyar ceton al’ummar jihar.

Fayemi yayi gwamnan jihar Ekiti tsakanin 2010 zuwa 2014, bai samu damar zarcewa a wa’adi na biyu da ya nema. Ya fadi ga Ayodele Fayose a zaben jihar da aka gudanar a cikin 2014.


Source: Tech

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *